Aƙalla mutum 200 sun mutu a wurin haƙar ma’adinai a Congo

0
1000497394
Spread the love

An ruwaito cewa sama da mutane 200 ne suka mutu sakamakon ruftawar wasu wuraren hakar ma’adanai a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Kakakin gwamnan lardin Arewacin Kivu da ‘yan tawaye suka nada, ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da masu hakar ma’adinai, da yara da mata.

Ya ce, an ceto wasu daga cikinsu.

Wurin yana samar da kusan kashi 15 cikin 100 na ma’adanin coltan na duniya, wanda yake da matuƙar muhimmanci ga samar da wayoyin hannu da sauran kayan lantarki.

Yana ƙarƙashin ikon ƙungiyar ƴan tawaye ta M23 tun shekarar 2024.

Mutane sama da miliyan ɗaya da rabi ne ke aiki a irin waɗannan wurare da ba a amince da su ba, inda haɗurra irin waɗannan suka zamo ruwan dare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *