Su waye ‘Kabilan Chamba dake yankin Kudancin Adamawa.

0
Exif_JPEG_420

Exif_JPEG_420

Spread the love

‘Kabilan Chamba dai na daga cikin ‘Kabilu 58 da Jahar Adamawa take dasu wanda kuma suke da zama a yankin Kudancin Adamawa tsakanin kananan hukumomin Mayo Belwa, Jada, Ganye da Toungo da kuma wani yanki na Jihar Taraba.

Sai dai Karamar hukumar Ganye, nan ne ke zaman tushen ‘yan kabilan Chamba kasancewar nan ne mazaunin Babban basarake mai daraja na 1 Gangwari Ganye Alh Umaru Adamu Sanda, wanda yake da zama a Ganye kuma ‘Yan kabilan Chamba na ganin sa da kima a matsayin Sarkin Chambawa na duniya baki daya.

Duk da cewa Yankin Masarautar Ganye ne tushen Chambawa amma kuma wani abin la’akari shi ne akwai ‘Yan kabilan Chamba a kasashen duniya daban daban kaman Jamhuriyar Kamaru, Ghana, da sauran su wadanda kuma suke tutiya da Garin Ganye a matsayin Helkwatar ‘Yan kabilan Chamba.

Sai dai kuma kaman yake a wadansu ‘Kabilun a ‘Kabilan Chamba ma akwai rassa daban daban dake bambanta su ta karin harshe, misali akwai Chamba-Leko, akwai Chamba-Dakka.

Akwai wasa da zolaya tsakanin ‘Yan kabilan Chamba da ‘Kabilun Mummuye, Jukun, Kuteb wadanda suke zaune lafiya a tsakanin su shekaru da dama da suka wuce.

‘Kabilan Chamba dai sunyi fice wajen Noman Gyeda da Doya kuma suna da fitattun mutane a duniya da sukayi fice kuma sukayi bajinta a matakan rayuwa daban daban kamar su Gen TY Danjuma, Major General Mayirenso Saraso, Hajiya Zainab Ahmed Kagara, Barr Bala Sanga, Alh Abdulmalik Yelwa, Hon Dominique Mapeo, Alh Faruq Jauro, Alhaji Adamu Sanda, Da dai sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *