Hukumar WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar WASSCE na 2025.

Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka ta 2025, WASSCE, ga ‘yan makaranta.
WAEC ta sanar da hakan ne a ranar Litinin a cikin wata sanarwa da ta fitar a hukumance ta X.
Hukumar shirya jarabawar yankin ta tabbatar da cewa dalibai da suka zana jarrabawar za su iya samun sakamakonsu ta yanar gizo.
“Majalisar jarrabawar Afirka ta Yamma tana farin cikin sanar da dalibai da suka zauna WASSCE daga Makarantu daban daban a 2025 cewa an fitar da sakamakon a hukumance a ranar Litinin, 4 ga Agusta, 2025,” in ji WAEC.
