Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da dashen bishiya miliyan biyar a jihar.

0
1000053162
Spread the love

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da dashen bishiyoyi miliyan biyar domin yaƙi da sauyin yanayi da inganta muhalli a jihar.

An ƙaddamar da gangamin dashen bishiyoyin ne ranar Lahadi a garin Yanbawa da ke yankin ƙaramar hukumar Makoɗa.

Sauyin yanayi da gusowar hamada wani abu ne da masana suka jima suna gargaɗi a kai tare da buƙatar ɗaukar matakan kariya.

Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da dashen, Gwamna Abba Gida-gida ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan gaggawa wajen kare muhalli da nuna muhimmancin dashen bishiyoyi wajen kariya daga gurɓata muhalli.

“Wannan gangami ba kawai batun dashen bishiya ba ne, abu ne da zai ingantan makomarmu, da kare yara masu tasowa daga illar gurɓacewar yanayi”, in ji shi.

Gwamnan ya kuma ce za a rabar da bishiyoyin miliyan biyar a faɗin ƙananan hukumomin jihar 44, domin dasawa a wurare muhimmai da suka haɗa da makarantu da masallatai da ma’aikatu da gonaki a birane da ƙauyukan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *