Fintiri ya karrama kocin Super Falcons Justine Madugu da gida da Naira miliyan 50 don nasarar WAFCON.

0
1754058067416
Spread the love

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya karrama kociyan kungiyar Super Falcons Justine Madugu da katafaren gida mai dakuna uku da kuma kyautar kudi naira miliyan hamsin da ya jagoranci kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata na shekarar 2025 (WAFCON) da aka gudanar a kasar Morocco.

Koci Madugu daga karamar hukumar Numan ya samu kyakkyawar tarba a gidan gwamnati dake Yola. Gwamna Fintiri ya yaba da kishin kasa, basirarsa, da kuma jagoranci, inda ya ce Najeriya ta lashe gasar WAFCON a karo na 10 a karkashin jagorancinsa.

Yayin da yake gabatar da kyaututtukan, Fintiri ya jaddada kudirinsa na bunkasa harkokin wasanni a jihar, inda ya bayyana ayyukan da ake gudanarwa kamar filayen wasanni na zamani.

Ya karawa Madugu kwarin guiwa da ya rika ba matasa hazikai a Adamawa.

Madugu ya nuna jin dadinsa da karramawar tare da bayyana kudurinsa na barin gado mai ɗorewa ga jiharsa, yana mai jaddada buƙatar ƙarin tallafi ga mata a fagen wasanni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *