Karancin abinci a sandanin ‘yan gudun hijira yayi sanadin mutuwar yara 13 a Sudan.

Yara 13 sun mutu a Sudan saboda rashin abinci.
Jami’an lafiya a Sudan sun ce yara 13 sun mutu sakamakon tsananin ƙarancin abinci a sansanin ‘yan gudun hijira da ke jihar gabashin Darfur.
Kungiyoyi likitoci a Sudan sun ce yanayin jin kai a sansanin Lagawa na ƙara tsananta inda rahotanni ke cewa ana samun ƙaruwar rashin abinci mai gina jiki musamman a tsakanin ƙananan yara.
Sansanin ‘yan gudun hijirar na ɗauke da aƙalla mutum 7,000, kuma yana fuskantar hare-hare daga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai akai-akai.
A farkon shekarar da muke ciki ne aka ayyana masifar yunwa a wasu sassan na Darfur inda mayaƙan RSF suka yi wa ƙawanya tsawon shekara guda.
