Allasane Ouatara zai sake tsayawa takara karo na hudu.

Shugaban ƙasar Ivory Coast Alassane Ouattara mai shekara 83, ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takarar zaɓen shugaban ƙasa karo na huɗu – wanda za a yi a ranar 25 ga Oktoba.
Sanarwar da ya yi a kafafen sada zumunta, na zuwa ne bayan da jam’iyyarsa ta Rally of Houphouëtists for Democracy and Peace (RHDP) ta amince da takararsa a hukumance.
A wani takaitaccen bayani da ya yi, Ouattara ya ce takararsa ta samo asali ne daga buƙatarsa ta kiyaye zaman lafiyar ƙasa a daidai lokacin da ta ke fuskantar kalubalen tsaro da na tattalin arziki.
Tuni dai shugabannin ‘yan adawa suka yi Allah-wadai da matakin, suna zargin cewa gwamnatinsa ta yi wa dokar zaɓe garambawul ne domin durkusar da manyan abokan hamayya.
Tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo, da tsohon Firaminista Guillaume Soro, da kuma tsohon minista Tidjane Thiam duk an cire saunayen su daga rajistar masu zaɓe, lamarin da ya hana su tsayawa takara.
Hankali ya ƙara tashi a yau bayan da hukumomi suka haramta zanga-zangar lumana da aka shirya yi a ranar 7 ga watan Agusta, ranar bikin samun ‘yancin kai na Cote d’Ivoire.
Ƙungiyoyin ‘yan adawa ne suka shirya zanga-zangar da nufin neman a gudanar da bincike mai zaman kansa kan jerin sunayen masu kaɗa kuri’a tare da mayar da sunayen waɗanda aka hana tsayawa takara.
Matakin na Ouattara ya yi nuni da wani gagarumin sauyi daga alkawuran da ya yi a baya na miƙa mulki ga sabbin shugabanni.
Har ila yau, ya kasance wani tunatarwa da tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaɓukan da suka gabata – ciki har da rikicin bayan zaɓen 2010-2011 wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 3,000, da tashin hankalin da ya biyo bayan yunkurinsa na neman wa’adi na uku a shekarar 2020.
Sama da masu jefa kuri’a miliyan 8.7 ne suka yi rajista don kaɗa kuri’a a zaɓen mai gabatowa.
Ƙungiyoyin fararen hula da shugabannin addinai, ciki har da ƙungiyar limaman cocin Katolika, sun nuna fargaba game da ƙaruwar rikice-rikicen siyasa, inda suka yi gargadin cewa za a iya samun sake ɓarkewar tashin hankali.
