Oluremi Tinubu ta taimakawa wadanda harin Benue ya shafa da kudi Naira Biliyan daya.

0
20250729_231730
Spread the love

Mai ɗakin shugaban Nijeriya, Remi Tinubu ta bai wa waɗanda rikicin jihar Benue ya ɗaiɗaita tallafin naira biliyan ɗaya, domin rage musu raɗaɗin da suka shiga.

Remi ta bayyana haka ne a yau Talata a gidan gwamnatin jihar ta Benue lokacin da ta kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummar jihar, bayan hare-haren da wasu suka kai garin Yelewata a watan Yuni – abin da ya janyo asarar rayuka sama da 100.

Remi ta ce an bayar da tallafin ne don taimakawa iyalai da aka ɗaiɗaita, sannan su kuma samu damar komawa muhallansu da farfaɗowa da kuma gina rayuwarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *