Hukumomin yankin Darfur na Sudan sun soki dakarun kasar bisa rashin nuna hazaka wajen kare yankin daga barazana.

Gwamnan yankin Darfur da ke Sudan ya soki sojojin gwamnati da gaza kawo karshen ƙawanyar da aka yi wa yankinsa wanda ya jefa al’ummar birnin El Fasher cikin matsananciyar yunwa.
Minni Minawi, ya kasance tsohon jagoran ƴan tawaye ne har yanzu kuma shi ke jagorantar wasu mayaƙa masu ɗauke da makamai waɗanda ke taimakawa sojojin ƙasar wajen kare birnin daga hannun mayakan RSF.
Sai dai duk da haka ana fama da yunwa a birnin inda kuma ba a iya shigar da kayan agaji.
Yanayin jin-kai a El Fasher na ƙara munana a kullum.
Mayaƙan RSF na ƙoƙarin ganin sun ƙwace ikon birnin fiye da shekara guda – inda suka hana shigar da abinci lamarin da ya jefa fararen hular birnin cikin matsananciyar yunwa.
Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan’adam da dama sun ce mayaƙan RSF na aikata kisan kiyashi da kuma kai hare-haren da ba su dace ba kan fararen hula da asibitoci.
