Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukan su sakamakon ambaliyan ruwa a China.

0
AFP__20250625__63PB83E__v3__HighRes__TopshotChinaWeatherFlooding-1750917405
Spread the love

Hoto – Reuters .

Aƙalla mutum 30 ne suka mutu a yankunan da ke wajen birnin Beijing sakamakon mummunar ambaliyar ruwa.

Wakilin BBC ya ce jami’ai sun ce kimanin ƙauyuka 130 ne suka kasance ba lantarki yayin da masu agaji ke amfani da jirage masu saukar ungulu don isa ga al’ummar da bala’in ya shafa kasancewar ruwa ya mamaye hanyoyi.

An kwashe mutane kimanin dubu 80 daga yankunan da ambaliyar ta mamaye, wanda hakan ya sa tuni Beijing ta yi babban gargaɗi game da ambaliyar.

Mamakon ruwan sama ne ya yi sanadiyar ambaliyar, wadda ta haifar da zabtarewar ƙasa – da tafiya da motoci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *