Gwamnan Sokoto ya bukaci jami’an tsaro su kawo ƙarshen ƴanbindiga a 2026

0
1000373459
Spread the love

Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya buƙaci mutanen jihar da su dage wajen bai wa jami’an tsaro goyon bayan domin magance matsalar hare-haren ƴanbindiga da jihar ke fuskanta ta hanyar taimaka musu da bayanan sirri da sauransu.

Gwamnan ya bayyana haka ne a saƙonsa na sabuwar shekarar, wanda mai magana da yawunsa Abubakar Bawa ya fitar, inda gwamnan ya ce za su ƙara ƙaimi domin ganin shekarar ta 2026 ta fi 2025 a kowane ɓangare.

“Za mu ci gaba da ba jami’an tsaronmu goyon bayan da suke buƙata domin samun nasara.

Mun riga mun fitar da tsare-tsaren da za mu yi musamman wajen tattara bayanan sirri da ganowa tare da daƙile hanyoyin da maharan ke bi wajen kai hare-hare musamman a ƙananan hukumomi 13 da ke fuskantar matsalar.

“Gwamna Aliyu gwamnatinsa za ta muhimmantar inganta ababen more rayuwa a jihar, “kamar yadda suke a ƙunshe a cikin muradunmu guda 9 Sannan za mu inganta sauran ɓangarorin lafiya da jin ƙai da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *