Sanata Abaribe ya koma ADC daga APGA

Sanata mai wakiltar Abia ta Kudu, Eyinnaya Abaribe ya fice daga jam’iyyar APGA, inda ya sanar da komawarsa jam’iyyar ADC ta haɗaka.
Abaribe ya koma jam’iyyar a rana ɗaya da tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar Labour, Peter Obi ya sanar da komawa jam’iyyar ta ADC.
A wata sanarwa da ADC ta fitar a shafinta na X, ta ce, “Sanata Eyinnaya Abaribe ya fice daga jam’iyyar APGA, sannan ya koma jam’iyyar ADC a hukumance.”
