Za mu zamanantar da Ilimin Almajirai- Gwamna Namadi

0
1000419712
Spread the love

Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya jagoranci wata tattaunawa ta musamman da malaman makarantun Tsangaya daga sassa daban-daban na Jihar Jigawa, a matsayin wani ɓangare na alƙawarin gwamnatinsa na gyara, da kuma sabunta tsarin ilimin almajirai a Jihar Jigawa.

Shirin, mai taken “Gwamnati Da Tsangaya” (Haɗin gwiwar Gwamnati da Makarantun Tsangaya), Hukumar Ilimi ta Jihar Jigawa ce ta shirya shi a matsayin wani taron ba da shawara da nufin zurfafa hulɗa tsakanin gwamnati da manyan masu ruwa da tsaki a fannin ilimin Alƙur’ani.

Shirin ya samar da dandamali ga malaman Tsangaya don tattauna abubuwan da suka faru, ƙalubale da ake fiskanta, yayin da kuma bayar da shawarwari masu amfani kan inganta walwala, ilimi, da kuma damar ɗaliban almajirai.

Wadanda suka halarci taron sun haɗa da shahararrun masu karatun Alƙur’ani daga sassa daban-daban na Jahar, waɗanda suka halarta a matsayin baƙi na musamman, wanda hakan ya ƙara jaddada muhimmancin gyare-gyaren Tsangaya na Jihar Jigawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *