Atiku ya yi maraba da komawar Peter Obi ADC

Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP kuma jigo a jam’iyyar ADC a yanzu, Atiku Abubakar ya ce yana maraba da komawar tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar Labour, Peter Obi cikin jam’iyyar ta haɗaka.
Atiku ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce komawar Obi jam’iyyar wani babban mataki ne mai muhimmanci a tarihin haɗaka a siyasar Najeriya.
“Ina maraba da komawar Peter Obi cikin jam’iyyar ADC a hukumance, wanda yake cikin ƙoƙarin da muke na samar da haɗaka mai ƙarfi da za ta ƙalubalanci jam’iyya mai mulki.
Jam’iyyar da za ta kafa mulkin da zai tabbatar da zaman lafiya da cigaban ƙasa.”Atiku ya ce yana fata komawar Obi cikin jam’iyyar za ta buɗe ƙofar da wasu waɗanda ya bayyana da ‘masu kishi’ za su biyo domin shiga jirgin haɗakar.
