Shugaban mulkin sojin Guinea Mamadi Doumbouya ya lashe zaben shugaban ƙasar

Shugaban mulkin sojin Guinea Mamadi Doumbouya ya lashe zaben da aka yi a karon farko a ƙasar tun bayan ƙwace mulki a 2021.
Sakamakon zaɓen ya nuna cewa shi ke da rinjaye a ƙuri’un da aka kaɗa abin ya nuna cewa ba za aje ga zagaye na biyu a zaɓen ba.
Masu sanya idanu daga ƙungiyar tarayyar Afirka sun bayyana zaɓen a matsayin sahihi wanda kuma aka yi shi cikin kwanciyar hankali.
To amma ƙungiyoyin farar hular da suka rinka kiraye-kirayen a dawo da mulkin farar hula sun bayyana shakku a game da batun cewa kashi 80 cikin 100 na masu kaɗa kuri’a sun fito sun yi zaɓe.
Doumbouya ya hambarar da gwamnatin shugaba Alpha Conde wanda ya jima a ka mulkin kasar shekaru hudu da suka wuce.
