Najeriya ta yi asarar kusan naira tiriliyan ɗaya sakamakon harajin Trump – NBS

0
1000389773
Spread the love

Najeriya ta yi asarar kusan naira biliyan 940.98 a fitar da kayayyaki zuwa Amurka a cikin watanni tara na farkon shekarar 2025 bayan ƙarin harajin shugaban Amurka, Donald Trump, kamar yadda bayanan Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) suka nuna.

Bayanan NBS sun bayyana cewa “Daga watan Janairu zuwa Satumba na 2025, Najeriya ta fitar da kayayyaki na kimar naira tiriliyan 3.65 zuwa Amurka, ƙasa da naira tiriliyan 4.59 da aka fitar a daidai wannan lokaci a 2024.”

Wannan na nufin an samu raguwar kashi 20.5 kenan.

Wannan koma-baya ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da sabon tsarin haraji inda shugaban Amurka, Donald Trump, ya ƙara harajin Najeriya daga kashi 14 zuwa kashi 15 cikin ɗari.

Harajin dai ya fara aiki ne a ranar 7 ga Agustan 2025 wanda ya fi shafar kayayyakin da ba na mai ba da Najeriya ke fitarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *