‘Tinubu ya gayyace ni da kansa in shiga APC’ – Gwamnan Filato Mutfwang

0
1000381097
Spread the love

Gwamnan Jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu da kansa ya gayyace shi ya fice daga Jam’iyyar PDP, ya koma APC mai mulki.

A cewarsa, bayan watanni na tattaunawa da kuma nazari kansa, dole ne ya dauki wannan matakin domin amfanin jihar.

Mutfwang, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis jim kadan bayan ya koma APC, ya ce bai dauki wannan matakin don neman riba ba, yayi ne don girmama Tinubu, wanda ya nuna sha’awa ta musamman ga Jihar Filato da kalubalenta.

Mutfwang ya bayyana karara cewa duk da cewa Shugaban ya mika masa gayyatar shiga APC a lokuta da dama, amma ya ki amincewa da hakan saboda yin nazari mai zurfi.

Ya lura cewa akwai kuma alamun manyan mutane, ciki har da sauran gwamnoni daga APC, amma a duk lokacin, ya tsaya kan shawararsa.

Duk da haka, ya bayyana cewa abin da ya canza ra’ayinsa a karshe shi ne kalubale da rudani a cikin PDP a matakin kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *