Fadar shugaban ƙasa ta musanta zargin amfani da EFCC wajen cin zarafin ’yan adawa

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta yi watsi da zargin da wasu ’yan siyasar adawa ke yi na cewa gwamnati na amfani da hukumar EFCC wajen cin zarafin masu adawa da gwamnati.
Fadar ta kuma musanta zargin cewa dimokuraɗiyya na cikin barazana saboda wasu manyan ’yan siyasa suna sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 14 ga Disamba, ya bayyana cewa waɗannan zarge-zargen yunƙuri ne na rikitar da al’umma domin neman riba ta siyasa.
Sanarwar ta ce wasu ’yan siyasar adawa na yin surutu ne kawai saboda gazawarsu a siyasa.
