Har yanzu sojojin Najeriya 11 na Burkina Faso – Tugga

Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya ce har yanzu sojojin Najeriya 11 na maƙale a ƙasar Burkina Faso bayan saukar gaggawa da wani jirgi da suke ciki ya yi a ƙasar.
Rahoton ya ce lamarin ya faru ne tun ranar 8 ga Disamba, lokacin da jirgin ya yi saukar gaggawa a ƙasar inda ƙungiyar ƙasashen Sahel (AES) ta zargi jirgin sojin Najeriya da keta sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izini ba.
A cewar rahoton, shugaban gwamnatin soji ta Mali, Assimi Goïta, ya bayyana saukar jirgin a matsayin matakin da ya saɓa wa ƙa’idojin ƙasashen duniya
Rundunar Sojin Saman Najeriya kuwa ta ce jirgin yana kan hanyarsa ce ta zuwa ƙasar Portugal lokacin da ya samu tangarɗar na’urar da ta tilasta masa yin saukar gaggawa a ƙasar.
Kungiyar AES – ta ƙunshi ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar wadanda suka fice daga ƙungiyar ECOWAS a watan Janairu, bayan takunkuman da aka sanya musu sakamakon juyin mulki a ƙasashensu.
Sun sanar da ficewarsu daga ƙungiyar ne a daidai lokacin da Najeriya ke jagorantar ECOWAS.
