Yadda kisan mata a Adamawa ke jan hankali a Najeriya

0
1000363100
Spread the love

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’Adama ta Amnesty Internaltional ta buƙaci a gudanar da bincike na gaskiya, domin hakkake abin da ya auku, dangane da zargin kisan mutum tara da raunata wasu da dama da aka yi, yayin da wasu mata suka gudanar da wata zanga-zangar lumana a garin Lamurde na jihar Adamawa, ta Najeriya, ranar Litinin da ta gabata.

Wannan kira ya biyo bayan zargin da ake ta yi ne, cewa sojoji ne suka buɗe wuta kan matan da ke zanga-zangar lumanar, amma kuma hukumomin sojan na musanta zargi.

Yanzu dai, baya ga alhini da zaman makoki da ake yi, an shiga ja-in-ja, dangane da wanda ake zargin ya yi harbin bindiga da ya kashe matan, kuma ya raunata wasu da dama, yayin da suke gudanar da zanga-zangar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *