CBN ya ƙara yawan kuɗin da ake iya cirewa a mako

Babban Bankin Najeriya (CBN) a jiya ya soke iyaka kan adadin kuɗin da ake iya ajiyewa a banki tare da ƙara kuɗin da ake iya cirewa daga naira 100,00 zuwa naira 500,000 a kowane mako.
Wannan canji ya fito ne a cikin wata sanarwa da bankin ya aika wa dukkan bankuna wacce Dr. Rita Sike, Daraktar Sashen Tsare-Tsaren Kuɗi da Dokoki, ta sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce daga 1 ga watan Janairu, 2026, za a yi amfani da waɗannan sabbin dokokin kuɗi a duk fadin Najeriya.
A bangaren injin cire kuɗi kuma, iyakar kuɗin da mutum zai iya cirewa zai kasance N100,000 a rana kuma N850,000 a kowane mako.
A cewar bankin, an yi sauye-sauyen manufofin ne da nufin rage tsadar sarrafa kuɗi da magance matsalolin tsaro da kuma daƙile haɗarin safarar kuɗi ba bisa ka’ida ba da ke da alaƙa da dogaro da mu’amalar kuɗi kai tsaye.
