Masu ruwa da tsaki sun haɗu don samun ingantaccen kiwon lafiya a Adamawa!

An gudanar da tattaunawa ta kafafen yaɗa labarai da ‘Yan Jarida, tare da masu ruwa da tsaki, gabanin kwanakin Riga-kafin Ƙasa na watan Disamba 2025 karkashin jagorancin Ƙungiyar (NIPDs) wanda UNICEF ta tallafa tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Lafiya a matakin Farko ta Jihar Adamawa (ASPHCDA), wanda ya gudana a Yola.
A cikin jawabin sa Daraktan Kula da Cututtuka da Rigakafi, Dr. James Vasumu, wanda ya yaba da muhimmiyar rawar da kafofin watsa labarai ke ci gaba da takawa wajen inganta lafiyar jama’a.
Shugaban Gudanarwa na ASPHCDA, Dr. Sulaiman Saidu Bashir, ya yaba da ƙoƙarin haɗin gwiwa da ya ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya a matakin farko a faɗin jihar kuma ya jaddada cewa ci gaban da aka samu a cikin ‘yan shekarun nan ba zai yiwu ba tare da tallafin jama’a da na kayan aiki da Gwamnatin Jihar Adamawa ta bayar a ƙarƙashin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ba.
Dr. Bashir ya nuna cewa jarin da jihar ta zuba ya ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya sosai, kuma da wannan tallafin, Adamawa yanzu tana da cibiyoyin kiwon lafiya sama da 80 a faɗin jihar.
A daya bangaren wakilan UNICEF, WHO, AFENET, da sauran manyan abokan hulda sun tabbatar da goyon bayansu ga kamfen ɗin allurar riga-kafi mai zuwa.
An gabatar da cikakken bayani game da NIPDs na Disamba 2025, waɗanda aka tsara daga 6 zuwa 9 ga Disamba, inda aka bayyana manufofi, dabaru, da kuma muhimmiyar rawar da al’ummomi ke takawa wajen tabbatar da cewa kowane yaro da ya cancanta ya sami digo biyu na Allurar riga-kafi ta baki.
