Gwamnan Bauchi ya miƙa ta’aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya bayyana marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin mutumin da ya damu da harkokin addinin musulunci, mai son zaman lafiya, da samar da fahimta da juriya tsakanin musulmai da mabiya sauran addinai.
A wani saƙon ta’aziyya mai ɗauke da sa hannun mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai, Muktar Gidado, gwamnan ya bayyana matuƙar baƙin ciki da alhinin rashin sannanen malamin addinin musuluncin.
Ya kuma ce ”Malamin babban abin kwatance ne a fannin koyar da addini, mutum ne me tsantsar imani, da basira da tawali’u.
Sheikh Dahiru Bauchi ya sadaukar da rayuwarsa wajen ɗabbaƙa addinin musulunci, da koyar da alQur’ani da kuma gina alumma”.
Gwamnan Bauchin ya ce jihar za ta ci gaba da martaba tarihin jagoran ɗarikar Tijjaniyyan ta hanyar yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da wanzuwar irin koyarwar sa da abin da ya yi imani da shi.
