Gwamnan Neja ya ce an ceto ƙarin yara 11 da ƴanbindiga suka sace a Papiri

Gwamnan jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya, Umar Bago ya tabbatar wa BBC cewa jami’an tsaro sun ceto ƙarin ɗalibai 11 na makarantar St Mary da aka sace.
A cewar sa ” A wani aiki na haɗin gwiwa tsakanin sojoji da sauran mutane, mun yi nasarar ceto yara 11 a wata gona”Sai dai gwamnan ya ƙi bayyana hanyoyin da suka bi wajen tantance waɗanda aka kuɓutar.
Ya kuma musanta cewa an sace yara sama da 300, inda ya ce makarantar ba ta bayar da bayanan da za a iya dogara da su ba, kuma sun buɗe makarantar ne duk da gargaɗin da jami’an tsaro suka yi.
Gwamna Bago ya ce jihar ta buɗe wani rijista a ƙaramar hukumar Agwara domin iyaye su rubuta sunayen ƴaƴansu da suka ɓace, amma zuwa yanzu iyaye 14 kawai su ka rubuta.
Ya kuma ce makarantun kwana a jihar da ke yankunan da ke da haɗari kamar Papiri, za su ci gaba da kasancewa a rufe har zai an kawar da duk wata barazana.
