Kungiyar matasa ta dakatar da ayyukan YEDC saboda rashin kyawun ayyuka a Adamawa

0
1000323859
Spread the love

Mambobin kungiyar masu rajin kawo sauyi a Najeriya sun dakatar da ayyukan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Yola, YEDC da karfin tsiya saboda gaza samar da wutar lantarki mai dorewa a jihar Adamawa.

A ziyarar da manema labarai suka kai harabar Yola Discos a ranar Litinin da misalin karfe bakwai na safe, mambobin kungiyar da yawa sun toshe dukkan hanyoyin shiga ginin dauke da takardu daban-daban suna nuna rashin amincewarsu da zargin rashin kyawun wutar lantarki ga gidaje a jihar.Da yake magana kan lamarin, wakilin hulda da jama’a na kungiyar.

Kwamared Musa Andrew ya ce kungiyar ta fito da cikakken karfinta don yin korafinta kan rashin wutan lantarki da ake bayarwa ga mazauna jihar.

Kwamared Andrew ya yi Allah wadai da cewa kungiyar ta yi kokari da dama a rubuce da sauran wasiku domin shugabannin YEDC su iya canza lamarin aikin su zuwa mai nagarta domin yawancin mazauna jihar ba sa samun isasshen wutar lantarki a gidajensu da wuraren kasuwancinsu.

A cikin jawabansu daban-daban, wasu mazauna yankin, ciki har da Ladi Demsa da Doris Elem, sun yi kira ga kamfanin rarraba wutar lantarki da ya inganta ayyukansu domin tabbatar da adalci da gaskiya, suna masu lura da cewa rashin kyawun ayyukan ya shafi kasuwancinsu sosai.

Kokarin da aka yi na samun martanin YEDC bai yi nasara ba har zuwa lokacin cike wannan rahoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *