Tinubu ya sanar da ceto mutum 38 da aka sace a cocin jihar Kwara

0
1000262560
Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da ceto masu ibada 38 da ‘yanbindiga suka yi garkuwa da su a cocin Eruku da ke jihar Kwara.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya kuma tabbatar da kuɓutar ɗalibai 51 cikin 315 da aka sace a jihar Neja.

“Godiya ga jami’an tsaronmu a ‘yan kwanakin nan, an ceto dukkan masu ibada 38 da aka yi garkuwa da su a Eruku na jihar Kwara,” in ji shi. Sai dai ba yi ƙarin bayani ba kan yadda aka ceto su.

“Ina ci gaba da bin halin da ake ciki kan yanayin tsaro a ƙasa baki ɗaya kuma ana ba ni bayanai akai-akai daga inda abubuwan ke faruwa,” in ji shi.

“Haka nan, ina mai farin ciki cewa an gano 51 daga cikin ɗaliban makarantar Catholic School ta jihar Neja.”

Tun da farko, ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya ta ce ɗaliban sun gudu ne daga hannun masu garkuwar tsakanin Juma’a da Asabar bayan sace su ranar Alhamis da dare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *