Sojojin Najeriya sun kama wani sanannen mai garkuwa da mutane a Taraba

Rundunar Sojan Najeriya ta 6, Sashe na 3, karkashin Operation Whirl Stroke, ta samu gagarumin ci gaba a cikin aikinta na Operation Zafin Wuta tare da kama wani babban mai garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo a karamar hukumar Wukari, jihar Taraba.
Sojoji sun kama Umar Musa Geyi a ranar 22 ga Nuwamba 2025 a Jandei-Kulamu bayan bayanan sirri masu inganci.
Geyi ya dade yana cikin jerin wadanda jami’an tsaro ke nema kuma yana da alaka da wata kungiyar garkuwa da mutane da ke aiki a yankin Wukari.
