Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun sakandiren jihar

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe duka makarantun sakandiren faɗin jihar saboda dalilai na tsaro da satar ɗalibai a wasu jihohi.
Kwamishinan ilimi na jihar Hon. Yusuf Sulaiman Jibiya ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ta ɗauki matakin ne saboda abubuwan da ke faruwa a maƙwabtan jihohi na satar satar ɗalibai.
”Kan haka ne muka ƙara tsananta matakan tsaron da muke ɗauka a makarantunmu, Bahaushe na cewa idan gemun ɗan’uwanka ya kama da wuta shafa wa naka ruwa”, in ji kwamishinan.
Ya ƙara da cewa rufe makarantun na wucin gadi ne, bayan komai ya daidaita za su umarci ɗaliban su koma makarantun domin rubuta jarrabawar ƙarshen zango, wadda ita ce dama yanzu ta rage.
Ya ce matakin ya shafi duka makarantun sakandire da ke faɗin jihar, ban da na furamare, kodayake ya ce su ma idan hali ya yi za su rufe su.
”Mun yi haka ne saboda ɗaukar matakan kariya, bai kamata ba kana jiyo matsala a nesa sannan ka tsaya ta ƙaraso inda kake”, in ji shi.
