Ƴan bindiga sun sace ɗalibai da Malamai a Jihar Neja ta Najeriya

0
1000312660
Spread the love

Ƴan ta’adda a Najeriya sun kai farmaki Makarantar St. Mary’s da ke ƙauyen Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara da ke Jihar Neja, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makaranta da ba a tantance adadinsu ba zuwa yanzu.

Rahotanni daga makarantar sun ce harin ya faru ne da tsakar dare, kuma tuni aka fara tattara bayanai domin gano yawan mutanen da aka sace.

Wata majiya daga cocin Katolika a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ta ce har yanzu ana tattara bayanai kuma za a fitar da sanarwa nan gaba.

Kawo yanzu Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ƴan Sandan Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce ana ci gaba da tattara bayanai, kuma daga bisani zasu fitar da cikakken bayani.

Shugaban sashen bada agajin gaggawa na ƙaramar hukumar Agwara, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da cewa ƴan ta’addan sun kutsa makarantar ne tsakanin ƙarfe 2:00 na dare zuwa 3:00 na dare, kuma a yanzu haka ana ci gaba da tantance adadin ɗalibai da ma’aikatan da aka yi garkuwa da su.

Wannan harin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan makamancinsa da ya faru a Maga, Jihar Kebbi, inda aka sace dalibai mata 25, lamarin da ya ƙara tabbatar da halin rashin tsaro da ƙasar ke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *