Gwamnatin sojin Nijar za ta gina kamfanin sarrafa albarkatun noma a Maradi

0
1000283118
Spread the love

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar janar Abdourahamane Tiani, ya sanar da aniyar gwamnati ta samarwa jahar Maradi wani katafaren kamfanin sarrafa albarkatun noman damina da na rani da ke lalacewa.

Gina wannan kamfanin zai laƙume kuɗin da suka kai CFA biliyan 60 domin bunkasa al’amuran noma a jahar Maradi.

Shugaban kungiyar ci gaban birni da karkara a ƙasar Alhaji Ali Kalla, ya ce wannan babban ci gaba ne a ƙasar kuma suna maraba da shi domin zai ƙara bunƙasa jihar ya ɗaga martabarta.

Ya ce kayyayakin da za a sarrafa sun haɗa da rogo, dankali, ayaba, da kayan lambu, da duk kayan da ake nomawa lokacin rani.

A baya ya ce manoma kan yi noman a adadi mara yawa, ko su yi saurin rabuwa da amfanin gonarsu saboda gudun lalacewa.

”Maradi dama abin a ta fi ba ƙarfi shi ne noma da kiwo da kasuwanci, wannan kamfani zai samar wa matasa aiki, ya basu damar faɗaɗa noma.” in ji shi.

Ali Kalla ya kuma ce ci gaba da kamfanin zai a kawo wa Maradi ya haɗa da samun na’uikan abinci daban daban, iya nomawa da sarrafa abin da ta noma a cikin gida har ma a aika wa wasu ƙasashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *