An fitar da Nnamdi Kanu daga kotu kan yin hargowa

Alkali a babban kotun tarayya da ke Abuja, inda ake zaman yanke hukunci ya buƙaci a fitar da wanda ake ƙara Nnamdi Kanu daga zauren kotun, bayan jagoran na IPOB ya nemi tayar da hargitsi ta hanyar yin hargowa.
Wanda ake ƙarar, kuma yake kare kansa bayan korar lauyoyinsa, ya soma hayaniya ne bayan alƙalin kotun ya soma jawabi.
Tun farko an bai wa Kanu damar yin jawabi na ƙarshe, sai dai a daidai lokacin da alƙali ya fara nasa jawabi, Kanu ya riƙa yin katsalandan, yana nuna adawa da kalaman alƙalin.
An buƙaci ya miƙa bututun maganar, amma ya ƙi, daga nan ne alƙalin ya buƙaci a yi waje da shi.
A yanzu dai an ci gaba da zaman shari’ar, kuma kotun ta ce za ta yanke hukuncin a bayan idon wanda ake ƙarar.
