Trump ya kare Yarima mai jiran gado na Saudiyya kan kisan Khashoggi

0
1000307375
Spread the love

Shugaban Amurka Donald Trump ya karɓi bakuncin Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman a ziyarar sa ta farko tun bayan kisan ɗan jaridar Jamal Khashoggi a 2018, inda Trump ya yi tsayin dakar cewa Yariman ba shi da masaniya kan kisan Marigayin.

A zantawar sa da manema labarai, Trump ya jadadda matsayarsa kan cewa Yariman ba shi da masaniya game da kisan, duk da cewa rahoton hukumomin leken asirin Amurka ya nuna cewa MBS ne ya amince da kamawa ko kuma kashe Khashoggi.

Wannan ziyara ita ce ta farko da MBS ya kai Fadar White House cikin fiye da shekaru bakwai, domin farfaɗo da martabarsa a idon duniya.

Rahotanni sun ce, yayin ziyarar an sanar da ƙasar Saudiyya a matsayin babbar abokiyar Amurka, wadda bata cikin NATO, sannan kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar sayen makamai, cigaban fasahar AI, da kuma ma’adanai masu muhimmanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *