DSS sun ce sun kama dillalin makamai a jihar Filato

Rundunar ‘yansandan farin kaya ta DSS a Najeriya ta ce ta yi nasarar kama wani dillalin makamai da ke yi wa ‘yanbindiga safara zuwa jihar Filato mai fama da rikicin ƙabilanci.
Cikin wata sanarwa a yau Lahadi, rundunar ta ce ta kama wanda take zargin a ranar Laraba bayan tattara bayanan sirri, kamar yadda shafin intanet na Channels TV ya ruwaito.
Ta ce bayanai sun nuna cewa mutumin yana haɗawa da kuma safarar makaman a unguwar Mista Ali da ke ƙaramar hukumar Bassa a jihar ta Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.
“Samamen ya ba mu damar kama mutumin mai suna Musa Abubakar, kuma ya amsa laifin haɗawa da safarar manyan makamai da harsasai ga ƙungiyoyin ‘yanbindiga a Filato da wasu jihohin arewaci,” a cewar sanarwar.
A ƙarshen makon nan rundunar ta sanar da sake kama Abdulazeez Obadaki, wanda aka fi sani da Bomboy, bayan ya tsere daga Gidan Yarin Kuje a Abuja wanda ake zargi da hannu a hari kan cocin Owo da ke jihar Ondo.
