Gomnatin mu na kokarin baiwa matasa hakkin su ta kowane bangare – Idris

Gwamnatin Tarayya ta ce Shugaba Bola Tinubu ya nuna amincewa da matasa ta hanyar ba su haƙƙoƙi na gaske da kuma damar da za su iya jagoranci.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana haka a taron matasa na APC Shiyyar Arewa maso yamma a Dutse, jihar Jigawa.
Mataimakinsa na Musamman kan Kafafen Yaɗa Labarai, Malam Rabiu Ibrahim, ya fitar da wata sanarwa game da jawabin ministan a taron, wanda aka bai wa manema labarai a ranar Litinin a Abuja.
A cewar sanarwar, ministan ya sake nanata alƙawarin gwamnatin tarayya na ƙarfafa matasan Najeriya ta hanyar shirye-shiryen kawo sauyi waɗanda ke haɓaka ilimi, samar da ayyukan yi, da kirkire-kirkire.
