Gwamnatin tarayya za ta kafa kamfanin sukari na miliyoyin daloli a Taraba

0
1000283552
Spread the love

Gwamnatin tarayya, ta hannun Majalisar bunkasa harkan Sukari ta Ƙasa, NSDC, ta fara shirye-shiryen kafa wani aikin samar da sukari na miliyoyin daloli a Jihar Taraba, da nufin haɓaka yawan amfanin ƙasa da kuma ciyar da Najeriya gaba wajen wadatar da kanta a fannin sukari.

Sakataren zartarwa kuma babban jami’in NSDC, Kamar Bakrin, ya jagoranci wata tawaga zuwa Jalingo, tare da rakiyar jami’an Lee Group, don neman goyon bayan Gwamna Agbu Kefas da Gwamnatin Jihar Taraba don wannan shiri.

Bakrin ya bayyana aikin a matsayin babban jarin da zai iya ƙara yawan samar da sukari a Najeriya, rage dogaro da shigo da kaya daga ƙasashen waje, da kuma haɓaka ci gaban tattalin arziki.

Ya jaddada cewa rawar da NSDC ke takawa ta haɗa da tallafawa masu zuba jari ta hanyar ba da kuɗi, nazarin yiwuwar aiki, horar da fasaha, bincike.

Bakrin ya kuma tabbatar da cewa Lee Group, ta hanyar reshenta na GNAAL Sugar, ta cika dukkan buƙatu a matsayin mai saka jari mai aminci tare da ƙarfin kuɗi da fasaha.

A martanin da ya mayar, Gwamna Agbu Kefas ya bayyana cikakken goyon bayan gwamnatin jihar, yana mai sake jaddada alƙawarin gwamnatinsa na ƙirƙirar yanayi mai kyau ga zuba jari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *