Charles Soludo ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra

0
1000282074
Spread the love

Hukumar zaɓen mai zaman kanta INEC ta sanar da Charles Soludo na Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba.

Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke babban birnin jihar, Awka a safiyar yau Lahadi.

Ya ce Soludo ya samu ƙuri’a 422,664, sai kuma Nichola Ukachukwu na Jam’iyyar APC mai biye masa da ƙuri’a 99,445.

George Moghalu na Jam’iyyar Labour ne ya zo na uku da ƙuri’a 10,576, sai Jude Ezenwafor na PDP mai ƙuri’a 1401.

Charles Soludo wanda tsohon shugaban babban bankin Najeriya ne, ya lashe zaɓen ne domin yin sake mulkin jihar a karo na biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *