An gudanar da zaman sulhu da ƴan bindiga a Katsina

Shugabannin ‘Yan bindiga sun yi alkawarin zaman lafiya mai dorewa bayan ganawa da al’ummomin Charanci da Batagarawa a Jahar Katsina.
Gwamnatocin kananan hukumomi na Charanci da Batagarawa a Jihar Katsina sun haɗu da takwarorinsu wajen shiga tattaunawar zaman lafiya da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke zaune a cikin dazuzzuka.
Taron zaman lafiya, wanda ya gudana a ranar Asabar, 8 ga Nuwamba, 2025, an gudanar da shi a garin Wurma na ƙaramar hukumar Kurfi a jihar Katsina.
A cewar wani rahoto da Militainment News ta tattara, taron ya samu halartar shugaban ƙaramar hukumar Batagarawa, Hon. Yahaya Lawal Kawo, wakilai daga ƙaramar hukumar Charanci, sarakunan gargajiya, da wakilan al’ummar Fulani mazauna dazuzzuka.
An ruwaito cewa zaman tattaunawar ya ƙare da kyakkyawan fata, yayin da wakilan ƙungiyoyin Fulani suka yi alƙawarin rungumar zaman lafiya mai ɗorewa da kuma zama lafiya da al’ummomin da ke makwabtaka da su.
