Ba za mu halarci taron G20 a Afirka ta Kudu ba “saboda ana kashe fararen fata a ƙasar” – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce babu wani jami’in kasarsa da zai halarci taron kasashe 20 masu arziki a duniya na G20 da za a yi nan gaba a cikin watan da muke ciki a Afirka ta Kudu.
A watan Satumbar da ya gabata ya sanar da cewa mataimakinsa JD Vance ne zai wakilici Amurka a taron, to amma yanzu ya tabattar da cewa babu wani jami’in gwamnatin Amurka da zai halarci taron.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta Mr Trump ya ce abin kunya ne a ce Afirka ta Kudu ce za ta karbi bakuncin taron.
Sannan ya kara nanata zargin da ake cewa ana kashewa ko kuma kwacewa turawa fararen fata ‘yan Afirka ta Kudu gonakinsu a kasar.
