Manyan hafsoshin tsaron Nijar da Mali da Burkina Faso sun gana a Niamey

Manyan hafsoshin tsaron ƙasashen ƙungiyar AES wato Nijar da Burkina Faso da Mali sun gana a Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar ƙarƙashin jagorancin shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Abdourahamane Tchiani.
Taron wanda aka yi a ranar 7 ga watan Nuwamba, ya mayar da hankali kan yunƙurin ƙarfafa haɗakar tsaro a tsakanin ƙasashen na ƙungiyar AES domin tabbatar da tsaronsu, kamar kamfanin dillancin labarai ANP ya ruwaito.
“Mun yi nisa wajen tattaunawa da duba yanayin tsaron ƙasashenmu da niyyar samar da haɗakar tsaro a tsakaninmu,” in ji ministan tsaron Mali Janar Sadio Camara.
Ya bayyana jin daɗinsa kan yunƙurin da suke yi, inda ya nanata cewa yana da ƙarfin gwiwar cewa za su samu nasara wajen tabbatar da tsaro a ƙasashensu.
A ranar 29 ga watan Janairu ne ƙasashen uku suka fice daga ƙungiywar Ecowas a hukumance, bayan suka zargi ƙungiyar da alaƙa da Faransa da wasu ƙasashen yamma, inda suka ƙafa ƙungiyar Alliance of Sahel States wato AES.
Yanzu dai ƙasashen sun fi ma’amala da ƙasar Rasha, sannan wasu sassansu na ci gaba da fama da matsalolin tsaro.
