Gwamna Buni ya gabatar da Kasafin Kudi na Shekarar 2026 sama da Naira Biliyan 515 ga Majalisar Dokoki

Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, ya gabatar da kasafin kudi na Naira Biliyan 515,583,000,000 na shekarar kasafin kudi ta 2026 ga Majalisar Dokoki ta Jihar.
An yiwa lakabi da Kasafin Kudi Na Ci Gaban Tattalin Arziki Da sake sabunta fannin gina ƙasa, wanda aka yi wa lakabi da kudin gudanar da ayyuka, kudaden gudanarwa da kuma kudaden ma’aikata.
Wannan ya yi hannun riga da Naira Biliyan 320,811,000,000 na shekarar da ta gabata.
Kasafin kudin ya samar da jimillar Naira Biliyan 192,128,000,000 wanda ke wakiltar kashi 37.3% na kudaden da ake kashewa akai-akai.
Jimillar Naira biliyan 323,455,000,000 wacce ke wakiltar kashi 62.7% na kasafin kudin an ware su ne don manyan ayyuka.
Gwamnan ya lissafa ayyukan kiwon lafiya, ilimi, noma da kuma ayyukan more rayuwa, ciki har da gina hanyoyi, wutar lantarki, samar da ruwa da sauransu, a cikin muhimman fannoni da gwamnati ta mayar da hankali a kansu a shekarar da ta gabata.
Gwamna Buni ya ce gwamnati za ta kafa cibiyar wankin koda wato dialysis a Gashua domin taimakawa masu fama da cutar koda “gwamnati za ta kuma gina sabon babban asibiti a Potiskum don rage cunkoso a asibitin kwararru” a shekarar 2026.
