2027: Gwamnan Nasarawa, Sule ya kori mataimaki saboda yakin neman zabe da wuri

0
1000271804
Spread the love

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya kori Babban Mai Ba shi Shawara Kan Ayyuka, Ahmed Seriki, saboda gazawarsa wajen bin umarnin da aka bayar kan yakin neman zabe kafin lokacin zaben 2027.

Babban Mai Ba da Shawara Kan Harkokin Jama’a ga Gwamna Sule, Mista Peter Ahemba, ya bayyana hakan a lokacin taron manema labarai na wata-wata a Cibiyar Ƴan jaridu NUJ da ke Lafia.

Ahemba yana amsa tambayoyi kan dalilin da ya sa Gwamna Sule ya dauki matakin duk da dokar da suka bayar amma suka ci gaba da nuna rashin amincewa duk da gargadin da aka yi masa na yakin neman zabe da wuri.

Ya ce gwamnan ya kori mataimakinsa wanda ya shiga yakin neman zabe a fili duk da gargadin da aka yi masa na akai-akai kan wannan aiki.

An ruwaito cewa an kori Seriki ne saboda ya tursasa gwamnan ya yi yakin neman zabe a fili don goyon bayan tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Abubakar, wanda ya nuna sha’awar tsayawa takarar kujerar gwamna a 2027.

Ya lura cewa gwamnatin jihar kwanan nan ta sami amincewar Gwamnatin Tarayya don gina gadar sama guda biyu da kuma hanyar karkashin kasa a Mararaba, Karamar Hukumar Karu ta jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *