‘Dan Majalisar Dokokin Amurka ya zargi Kwankwaso da hannu a kisan kiyashin Kiristoci a Najeriya

0
1000269070
Spread the love

Wani ɗan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya zargi tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da hannu a kisan Kiristoci a Najeriya.

Moore ya yi zargin ne bayan martanin Kwankwaso ga rahotannin shirin shiga tsakani na sojojin Amurka a Najeriya.

Da yake magana a shafukan sada zumunta, Moore ya yi tambaya game da tarihin tsohon gwamnan, inda ya rubuta: “Gwamna, shin kana son yin tsokaci kan hannunka a mutuwar Kiristoci? Ka kafa dokar Shari’a. Ka sanya hannu kan dokar da ta sanya abin da ake kira sabo a matsayin hukuncin kisa.

“Kwankwaso, wanda ya yi aiki a matsayin gwamnan jihar Kano lokacin da aka aiwatar da dokar Shari’a a watan Nuwamba na 2000, ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan kan yanayin tsaron Najeriya.

A cikin sanarwarsa, Kwankwaso ya gargadi Amurka game da daukar mataki na, yana mai bayyana Najeriya a matsayin kasa mai ‘yancin kai da ke fama da barazanar tsaro da ta shafi addinai da kabilanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *