NSCDC ta kama babbar mota cike da bututun NNPC da aka sace a Adamawa

0
1000266990
Spread the love

Rundunar tsaron farin kaya ta NSCDC reshen Jihar Adamawa ta kama wata babbar mota da ake zargin tana dauke da bututun kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC).

Kwamandan NSCDC a Adamawa, Idris Bande, ya ce kamawar ta biyo bayan bayanan sirri daga mazauna yankin.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin a ranar Litinin a Yola.

Kwamandan ya bayyana cewa motar da aka kama ta dauke da bututu sama da 200 da ake zargin mallakar NNPC ne, ya kara da cewa manajan depot na kamfanin na Adamawa ya tabbatar da mallakar kayayyakin.

Ya kuma tuna cewa kimanin makonni uku da suka gabata, rundunar ta kama wata babbar mota dauke da bututun NNPC sama da 300.

A cewarsa, an kammala bincike kan lamarin da ya faru kwanan nan kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

Bande ya gargadi wadanda ke da hannu a satar da lalata kadarorin gwamnati da su daina ko kuma su fuskanci fushin doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *