An girke tarin jami’an tsaro a sakatariyar jam’iyyar PDP

An girke jami’an tsaro a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Abuja, yayin da mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar arewa ta tsakiya, Abdulrahman Mohammed a matsayin shugaban jam’iyyar na riƙo, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.
Kwamitin gudanarwar jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Samuel Anyanwu, ne ya sanar da naɗin Mohammed bayan dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Damagun.
Rikicin babban jam’iyyar hamayyar Najeriyar ya ta’azzara bayan da a ƙarshen mako, shugaban jam’iyyar na ƙasa, Iliya Damagum da wasu mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar suka sanar da dakatar da babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Samuel Anyanwu da wasu ƴan kwamitin
Lamarin da ya sa ɓangaren Anyanwu ya mayar da martani ta hanyar dakatar da Damagum da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar da wasu mutum huɗu.
