An rantsar da Samia Saluhu Hassan a wa’adin mulkin Tanzaniya na biyu

An rantsar da Shugaba Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya.
Cikin wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin tsaurara matakan tsario a Dodoma, babban birnin ƙasar an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bar mutane da dama sun halarta ba.
Baƙin da aka gayyata ne kawai aka bai wa damar zuwa wurin, yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar, sakamakon rikicn zaɓe da aka samu a ƴankwanakin nan.
Shugaba Samia ta lashe zaɓen da aka gudanar a makon da ya gabata da kashi 98 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.
Sai dai ƴan hamayya sun yi watsi da sakamakon a matsayin magudi.
