Hukumar NCC ta wayar da kan masu shagon littattafai a Adamawa

0
1000264917
Spread the love

Hukumar Kula da Haƙƙin mallaka ta Najeriya (NCC) ta gudanar da kamfen ɗin wayar da kan jama’a na shekara-shekara kan hatsarori da rashin bin ƙa’ida ga masu shagunan littattafai a jihar Adamawa.

Mai riƙon ƙwarya na NCC, Mista Yusuf Ibrahim, yayin da yake jagorantar tawagarsa zuwa shagunan littattafai daban-daban a Jimeta-Yola a ƙarshen mako, ya nuna godiyarsa ga himmar da masu shagunan littattafai suka nuna wajen bada hadin kai a duk lokacin da Hukumar ke son yin mu’amala da su don inganta masana’antar.

Yusuf da tawagarsa sun zagaya sun wayar da kan masu shagunan littattafai ta hanyar ziyartar shagunansu don sanar da su cewa hukumar tana harabar kasuwancinsu don duba da sa ido kan kayyyakin su da nufin kare kadarorin masu mallakarsu na asali waɗanda suka yi aiki tuƙuru kuma suka buga littattafansu bisa doka.

Yana kara kiran su dasu guji duk wani aikin da zai taka doka na hakkin mallaka yana gargadin cewa akwai tsauraran takunkumi ga waɗanda suka ƙi bin ƙa’idodi musamman waɗanda ke da niyyar da ba ta dace ba, yana mai gargaɗin cewa doka zai same su.

A cikin martaninsu daban-daban, masu shagunan littattafai kamar Mr.Ekene Ofojitu na Great Achievers Bookshop, Osita Augustine Okafor na Bright Austin Bookshop da Mr.Chibuke Anselm na Tropical Bookshop Ltd. sun yi maraba da aikin, suna mai cewa zai ƙara wa masana’antar kima.

NCC ta duba kuma ta wayar da kan mutane fiye da goma daga shahararrun shagunan littattafai a kan titin Bishop, hanyar Galadima Aminu da kuma cikin kasuwar Jimeta Ultra Modern da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *