Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara har yanzu yana cikin PDP – Jakada Mubi

Hasashe da ke yawo a kafafen yada labarai na cewa Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC ba gaskiya ba ne.
Wani makusancin Gwamna, Alhaji Fahat Jakada Mubi shi ne ya karyata ikirarin a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa kuma ya fitar a Abuja.
A cikin sanarwar, Jakada ya bayyana cewa, Gwamna Dauda Dare yana halartan taro a Abuja kuma ya kasance bako mai jawabi ga mahalarta Kwas na Gudanar da Leken Asiri na Shugaban Kasa (EIMC) 18 ranar Laraba a Cibiyar Nazarin Tsaro ta Kasa da ke Abuja kuma ba tattaunawar siyasa ba ce ta kai shi.
Jakada ya bayyana wannan jita jitan a matsayin “wani yunƙuri na ƙirƙirar ruɗani daga waɗanda Gwamna Dare ya mayar da su marasa aikin yi tun lokacin da ya hau mulki a 2023, musamman tare da kyakkyawan aikinsa na mayar da jihar Zamfara cikin yanayi mai kyau a tsakanin sauran jihohi.
Don haka Jakada ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da irin waɗannan labaran ƙarya da masu yin kutse ke yi waɗanda masu biyan albashi ke ɗaukar nauyinsu don samun riba ta siyasa, yana mai lura da cewa Gwamna Dauda Lawal Dare ya ci gaba da mai da hankali kan isar da ayyuka masu ma’ana kai tsaye ga ‘yan jihar Zamfara.
