Trump ya soke bizar shiga Amurka ta Wole Soyinka har abada

0
1000253354
Spread the love

Gwamnatin Amurka a karkashin Shugaba Donald Trump ta soke takardar izinin shiga kasar daga Farfesa Wole Soyinka, wanda ya lashe kyautar Nobel kuma marubuci a duniya.

Soyinka ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Kongi’s Harvest Gallery, Freedom Park, Lagos Island, inda ya yi wa manema labarai jawabi kan batun.

Soyinka ya ce bai san wani laifi da zai iya haifar da soke takardar izinin shigan ba ind ya nuna cewa matakin da gwamnatin Amurka ta dauka bai dace ba.

Mai lambar yabo ta Nobel ya kara da cewa ya sami sanarwar janye takardar shiga kasar daga Ofishin Jakadancin Amurka, yana mai cewa yanzu ba zai iya tafiya kasar ba.

A cewarsa, an sanar da wannan lamari ta hanyar wata wasika ta hukuma, kodayake ba a bayar da takamaiman dalili na daukar matakin ba.

Farfesa ya kara da cewa ya fara tunani kan ko wani daga cikin ayyukansa na baya ne ya haifar da hakan.

Soyinka, ɗaya daga cikin fitattun marubutan adabi a Afirka, ya daɗe yana da kyakkyawar alaƙa da hukumomin ilimi da adabi ta Amurka, wanda hakan ya sa soke dokar ya ba wa masu lura da al’amura mamaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *