Paul Biya ya lashe zaɓen shugaban Kamaru

Shugaban ƙasar Kamaru mai ci Paul Biya ya lashe zaɓen shugaban ƙasa karo na takwas.
Majalisar Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ce ta bayyana Paul Biya, mai shekara 92 a duniya a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Wannan na nufin Biya zai ci gaba da jan ragamar ƙasar har zuwa shekara ta 2032.
Biya ya lashe zaɓen da kashi 53.66% na ƙuri’in da aka kaɗa, inda ya samu ƙuri’a sama da miliyan biyu, sai kuma jagoran adawar ƙasar, Issa Tchiroma Bakary ke biye da shi, inda ya samu kashi 35.19%, sama da ƙuri’u miliyan ɗaya.
