Matasa biyar sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Gombe

Akalla ‘yan mata matasa biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin ruwa a garin Nafada, jihar Gombe.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa wadanda abin ya shafa sune Najib Ibrahim, mai shekaru 18; Hauwa’u Dogal, mai shekaru 15; Ummati Baraya, mai shekaru 16; Umaira Gidado, mai shekaru 16; da Amina Jaliya, mai shekaru 15.
Gwamnan jihar, Inuwa Yahaya, ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ismaila Uba-Misilli, a ranar Lahadi, ya bayyana matukar bakin ciki game da lamarin a cikin sakon ta’aziyya ga iyalan da suka rasu yana tausayawa iyayensu da kuma dukkan al’ummar Nafada.
A cewarsa, rashin ba wai kawai abin takaici ne ga iyalan ba, har ma da dukkan jihar.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya yiwa mamatan rahama, ya kuma ba iyalansu ƙarfin jure rashin, yana mai jaddada buƙatar bin ƙa’idodin kiyaye lafiyar sufuri na ruwa don hana afkuwar haɗari a nan gaba.
Ya kuma yi kira ga majalisun ƙananan hukumomi, shugabannin al’umma, masu gudanar da jiragen ruwa, da masu kula da su da su aiwatar da ƙa’idojin tsaro a yankunan da ke gabar kogin.
Yahaya ya umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha da Majalisar Karamar Hukumar Nafada da su tallafa wa iyalan da abin ya shafa.
